Hare Haren Jiragen Sama Da Saudiyya Ta Jagoranta Sun Tafka Barna

Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta kasa da kasa ta ce hare-haren jiragen saman da Saudiyya ta jagoranta a Yemen sun rutsa da wasu gine-ginen kasuwanci da dama, a tashe-tashen hankulan da aka shafe shekara guda ana yi, wadanda su ka yi sanadin mutuwar mutane 130 wasu kuma daruruwa su ka rasa abin yi.

A wani rahoton da ta fitar jiya Litini, kungiyar ta Human Rights Watch ta ce wuraren sana'o'in da aka lalata sun hada da na kamfanoni da wuraren adana kayan sayarwa da kuma tasoshin samar da makamshi, wanda ke taimakawa wajen sarrafawa da adanawa da kuma rabar da kayan abinci da kuma magunguna da kayan lataroni.

Kungiyar ta ce 10 daga cikin hare-haren da aka kai kan kamfanonin da alamar laifuka ne saboda babu muradun sojoji a wuraren. Ta ce wasu daga cikin irin wadannan hare-haren ma na iya zama laifukan yaki.