Harin al-Shabab Ya Halaka Mutane 4 Tare da Jikata Wasu 10 a Somalia

Ma'aikatan kiwon lafiya na taimakawa wanda ya jikata a harin na jiya

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Somalia ya tabbatar cewa harin da al-Shabab ta kai kan Mogadishu babban birnin kasar ya halaka akalla fararen hula hudu tare da jikata wasu 10

A Somalia ma, akalla fararen hula biyar ne suka rasa rayukansu, sannan wasu sama da goma suka jikkata, bayan da mayakan Al Shabab suka harba makamai a wata unguwar fararen hula da ke Mogadishu, babban birnin kasar.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar, Abdulaziz Ali, ya tabbatarwa da Sashen Somaliya na Muryar Amurka cewa, an samu asarar rayukan ne sanadiyar makaman da aka harba.

Wani kwararre a fannin tsaro a Mogadishu, ya fadawa Muryar Amurka cewa, makaman da aka cilla guda uku, masu girman ma’aunin mili-mita 60, sun fada a unguwar fararen hula ne a Gundumar Wadajir da ke kusa da hedkwatar rundunar dakarun Tarayyar Afirka mai aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia, wacce ake kira AMISON a takaice.

Tuni dai kungiyar ta Al Shabab, ta dauki alhakin kai wannan hari, wanda ya faru a jiya Lahadi, inda ta tabbatar da cewa niyyar ta ita ce, ta kai harin kan dakarun na Afirka.