Harin da aka kai Ivory Coast yunkurin tarwatsa cigaban da kasar ta samu ne - inji Pham

Grand Bassam Resort Ivory Coast wurin da aka kai hari jiya Lahadi

Wani kwararre a a Afrika ya ce ya kamata a dauki harin da aka kai akan kasar Ivory Coast a matsayin wani yunkuri na kungiyar Al Qaeda na ganin ta haifar da husuma yayin da kasar ke samun karuwar zaman lafiya musamman a fannin siyasa.

Darektan wata cibiyar da ake kira Atlantic Council mai hedkwata a nan Amurka, wato J. Peter Pham, ya ce zai zama abin takaici idan har kungiyar Al Qaeda ta wargaza duk ci gaban da kasar ta Ivory Coast ta samu cikin shekaru hudu.

Ya kara da cewa akwai bukatar Amurka da Faransa da ta raini kasar, da su himmatu wajen kai dauki ga duk kasasshen da suke kokarin taimakon kansu.

A cewar Mr Peter, wannan hari da kungiyar ta Alqaeda ta kai, mummunan abu ne kuma ya kamata kowa da kowa ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya kara da cewa harin ya nuna karara irin mugum nufin kungiyar ta Al Qaeda a yankin Maghreb.

Kwararren ya kara da cewa bai yi mamaki ba da kungiyar ta kai hari Ivory Coast, domin tun bayan da Faransa ta kai dauki wa kasar Mali, akwai fargabara cewa kungiyar ta Al Qaeda za ta fadada hare-harenta a yankin Sahel domin ta nuna karfinta.