Harin da Aka Kai Kan Jami'ar Amurka dake Kabul Ya Hallaka Mutane 10

Wasu cikin wadanda harin na Kabl ya rutsa dasu

Rundunar ‘yansanadan Afghanistan tace mutane akalla 10 aka kashe, wasu fiyeda 37 suka ji rauni a cikin wani mummunan harin da aka dauki sa’oi 10 ana kaiwa akan Jami’ar Amurka dake birnin Kabul, wanda sai yau Alhamis aka zo karshensa.

Wadanda aka kashen sun hada da dalibbai 7, ‘yansanda 2 da kuma wani dogari 1. Akwai kuma wani malami dan kasashen waje a aickin wadanda aka yi wa rauni, a cewar kakakin ma’aikatar harakokin cikin gida, Sediq Seddiqi.

Mutane sama da 700 da suka hada da dalibbai da malamansu aka yi nasarar fitowa da su daga cikin jami’ar, inji kwamishinan ‘yansandan birnin na Kabul, Rahman Rahimi.

Wasu daibai da sukka jikata

An soma kai wannan harin ne da misalin karfe 6.30 na marecen jiya Laraba lokacinda aka fasa wani bam, wanda aka biyo bayansa da harbe-harbe.

‘Yansanda sunce an kashe akalla 2 daga cikin maharan.Har zuwa yanzu dai ba wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.