Harin jirgin sama a Syria ya yiwa wani kwamandan mayakan ISIS mummunan rauni

Tarkhan Batirashvili kwamandan ISIS da ya samu mummunan rauni

Wata tawagar masu sa ido kan rikicin Syria ta ce an an jiwa daya daga cikin shugaban mayakan IS mummunan rauni bayan wasu hare-haren sama da aka kai a makon da ya gabata.

Tawagar wacce ta fito daga kungiyan nan mai sa ido kan rikicin Syria, ta musanta rade-radin da ake na cewa an kashe Tarkhan Batirashvili, wanda ake wa inkiya da Abu Omar Al- Shishani ko kuma Omar dan Chechen.

Tawagar masu sa idon ta kara da cewa an garzaya da Al Shishani zuwa tungar mayakan ta IS da ke Raqqa domin ayi masa magani.

Jami’an tsaron Amurka sun bayyana cewa watakila an kashe jagoran mayakan a hare-haren da aka kai a kusa da arewa maso gabashin garin Al Shaddadi.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta gayawa Muryar Amurka ranar Talata cewa, Al Shishani ya kai ziyara yankin ne domin yin nazarin karfin dakarunsu tare da karfafa musu kwarin gwiwa, bayan da suka rasa wasu yankunansu ga dakarun Syria da ke samun goyon bayan Amurka.