Harin Kunar Bakin Wake A Janhuriyar Nijar

  • Ibrahim Garba

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Wasu motoci shake da bama-bamai sun tarwatse a mashigar barikin soja a garin Agadez da garin Arlit, inda mutane 19 su ka mutu.
Wasu motoci dankare da bama-bamai sun tarwatse a mashigar barikin sojan garin Agadez da garin Arli, in mutane kimanin 19 su ka riga mu gidan gaskiya, baya ga da dama da su ka sami raunuka.

Wakilin Muryar Amurka a Nyamai, Abdoulaye Mammane Amadou ya ruwaito wani ganau mai suna Malam Bashir Lawal mazaunin kusa da inda aka kai harin a garin Agadez na cewa sun tashi sallar asuba kenan bama-baman su ka tashi. Daga nan kuma aka shiga musayar wuta har zuwa wajen karfe takwas na safe.

Haka zalika, babban Magajin Garin Arlit, Mauli Abdurrahman, ya gaya wa wakilin namu cewa bama-baman sun yi kaca-kaca da jikunan mutanen da su ka mutu, sannan wasu da dama sun sami raunuka. A cewar wakilin namu, 'yan kunar bakin waken sun so ne su kutsa cikin wata ma'aikatar da ke daura da wurin.

Your browser doesn’t support HTML5

Harin Kunar Bakin Wake A Janhuriyar Nijar,'-2:38'