Harkokin Ilimi Na Kara Tabarbarewa a Jamhuriyar Nijar

Daliban Nijar da suka yi zanga zanga

Bayan kai ruwa rana da aka yi tsakanin hukumomin ilimi da malaman 'yan makaranta da dalibansu da aka yi, da alamu tsugune bai kare ba

Kawo yanzu dai alamuran ilimi sai dada tabarbarewa suke yi saboda yajin aikin da malaman keyi yaki ci yaki karewa.

Wasu dalibai da aka zanta dasu suna cewa haka aka yi shekarar da ta wuce yanzu kuma suna cigaba da zama a gidajensu babu karatu. Sun ce suna baya matuka a karatunsu. Sun kira mahukumta da malamansu su gaggauta su samo bakin zaren warware matsalar.

Daliban suna son su koma karatu domin gaba sboda, a cewarsu idan basu samu karatun ba wannan karon to kowa ma zai koma baya. A cewar wani daliin iyayensu sun zuba kudi cikin karatunsu idan kuma basu yi ba tamkar hasara ke nan iyayensu suka yi.

Su ko iyayen yara matsalar ilimin ta fi ci masu tuwa a kwarya. Su iyayen sun koka. Suna cewa su talakawa ne. Babu inda zasu kaisu karatu. Gwamnati ce take taimaka masu amma kuma tayi watsi dasu. Suna tsoron kada 'ya'yansu su shiga yawon banza suna shaye-shaye su zubar da tarbiyarsu. Suna rokon gwamnati tayi abun da ya kamata.

Sai dai hukumomin ilimi sun lashi takobin magance matsalarkamar yadda Ministan ilimi ya shaida. To amma Malam Yau magatakardan malaman makaranta 'yan kwantiragi yace ba nan gizo ke saka ba. Yace inda mahukuntan koli sun shiga harakar gadan gadan da yanzu an warware matsalar.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Harkokin Ilimi Na Kara Tabarbarewa a Jamhuriyar Nijar - 3' 49"