Hasashen Masana Kan Tattalin Arzikin Najeriya a 2019

Lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke gabatar da kasafin kudin 2019 a gaban majalisar dokokin kasar, a Abuja, ranar 19 ga watan Disamba, 2018.

Masana sun ce tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a wannan shekara, sai dai akwai yiwuwar ya fuskanci dan tarnaki saboda zabe na gama-gari da ke tafe.

Najeriya na shirin yin zaben shugaban kasa a watan Fabrairun, lamarin da masanan suka ce zai sa masu zuba hannayen jari na ciki da wajen kasar su dakata da zuna hannayen jari.

“Gaskiya ne akwai cewa za a samu ci gaba a tattalin arzikin kasa, koda yake, abin da zai dan shafi abin shi ne, zaben da za a yi 2019, zai dan sa wadanda za su saka hannun jari a kasar su dan ji dar-dar.” In ji masanin tattalin arziki ta fuskar siyasa, Malam Isa Imam.

Imam wanda har ila yau wakili ne a kungiyar tattalin arziki ta Najeriya, ya kara da cewa, “amma da zaran an gama zaben, aka tabbatar da gwamnati, abubuwa za su (ci gaba da)” tafiya.

A cewar Imam, akwai tsare-tsare da gwamnati ta tanadar a cikin kasafin kudin bana, wadanda suka shafi fannin noma, kananan masana’antu da kuma fannin saka hannayen jari da ba da tallafi.

Ba dai kasafai za ka ji ‘yan Najeriyar na bayyana cewa su na ganin bunkasar tattalin arzikin ba, amma dai wasu ‘yan kasuwa na da ra’ayin cewa farashin wasu kayayyakin masarufi sun sauka.

“Shekarar bana sai dai a ce alhamudulillahi, ba kamar shekarar da ta gabata ba, abubuwa da dama an samu saukinsu, kamar irinsu su shinkafa, siga, da su masara gaskiya sun sauka sosai tsakani da Allah.” In ji wani dan kasuwa mai suna Musa Suleman a Legas.

Amma ba a rasa wadansu da ke da ra’ayin cewa, farashin na kayayyaki ba sa sauka, asali ma tashi suke yi.

Su dai bangaren 'yan adawa a kasar, na kokawa da yadda ake tafiyar da harkokin tattalin arzikin na Najeriya, inda suke ikrarin har yanzu babu wani sauyi da aka samu.

Batun canza kudaden ketare irinsu dala na daga cikin abubuwan da ‘yan adawan ke cewa na kawo tarnaki wajen bunkasar tattalin arzikin Najeirya, kamar yadda dan takarar shugaban kasa karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya fada a hirar da ya yi da Sashen Hausa.

“Ya za a yi a ce yau farashin dala na da matakan farashi wajen hudu ko biyar? Wani a ce ya saya 300, wani ace ya saya 305, wani 310, ya za a yi a karfafa naira, ba zai yi wu ba." In ji Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne.

Ya kara da cewa, "in ni ne shugaban kasa, sai na hada (farashin) duk wuri guda, duk sai su zama farashi guda, saboda 'yan kasuwa na ciki da da waje kowa ya san lallai ga yadda farashin yake."

Sai dai shugaba mai ci, Muhammadu Buhari wanda zai kara da Atiku a zaben na watan Fabrairu, ya ce, lissafin da suka yi na bunkasa tattalin arzikin kasar ya ta'allaka ne akan kasafin kudin bana.

"Inda muka nufa din nan, mun saka shi ne a lissafin tono mai ganga miliyan 2.3 akan dalar America 60 kuma akan kowacce dala naira 305." In ji Buhari.

Ya kara da cewa, "tafiyar da gwamnati, dole a nunawa mutane hanyar da za a bi a samu kudin da kuma yadda za a kashe kudin, kuma mun nuna batun hanyoyi da tsaro da biyan ma'aikata akan wannan."

Saurari wannan rahoton na Babangida Jibril domin jin cikakken bayani da kuma yadda shawara da aka ba jama’a domin bunkasa hanyoyin shigar kudadensu, da kuma tsokacin da ‘ytan kasuwar kasar wajen ke yi kan tattalin arzikin na Najeriya:

Your browser doesn’t support HTML5

Hasashen Masana Kan Tattalin Arzikin Najeriya a 2019 - 4'49"