Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Halaka Mutum 94 A Iraqi

Wasu 'yan uwan wadanda ke cikin jirgi suna dako a bakin Kogin Tigris

Akalla mutane 94 suka mutu a lokacin da wani jirgin ruwan fasinja da aka laftawa kaya fiye da kima, ya nutse a Kogin Tigris a kusa da birni Mosul da ke Iraki.

A jiya Alhamis jami’ai sun ce sama da mutum 180 ne a cikin jirgin, yayin da suke bukuwan sabuwar shekarar Kurdawa, da ake wa lakabi da “Nowruz,” da kuma Ranar tunawa da Mahaifiya.

Da yawa daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su mata ne da kuma kananan yara da suka yi ta kokarin yin iyo a igiyar ruwa mai tafiya da sauri.

Shi dai Kogin Tigris, wanda aka fi saninsa da tafiya a hankali, yana kwarara ne da sauri kuma ya cika ya tumbatsa, saboda ruwan sama da aka yi da kuma dusar kankara da take narkewa daga tsaunukan kasar Turkiyya take kwarara cikinsa.

Jami’ai sun kuma gargadi mazauna birnin Mosul cewa ana tsammanin ruwan Kogin zai ciko, saboda an sako ruwa daga wani dam da ke kusa.

Yayin da ‘yan uwa da iyalai ke jiran karin haske game da wannan hadarin jirgi, akwai fargabar cewa adadin wadanda suka mutu ya karu.