Hidimomin Tunawa Da Bakin Haure A Duniya

Yayin da ake shirin hidimomin tunawa da ranar bakin haure ta duniya a gobe Talata 18 ga watan Disamba,kungiyoyin kare hakkin ‘yan ci rani a Jamhuriyar Nijar sun shirya wata mahawara.

Yayinda ake shirin hidimomin tunawa da ranar bakin haure ta duniya, a gobe Talata 18 ga watan Disamba, kungiyoyinn kare hakkin ‘yan ci rani a Jamhuriyar Nijer, sun shirya wata mahawara domin tattaunawa akan koma baya, da batun yaki da kwararar bakin haure ya haddasawa ‘yan cin kai da kawo jama’a Nafiyar ta Afirka.

Amandine Bach, mai ba da shawara a fannin siyasa wa bangaren masu sassaucin ra’ayi a majalisar Turai, tana mai bayani wa mahalarta mahawarar da kungiyoyin kare hakkin bakin haure suka shirya, domin nazarin matsalolin da siyasar Turai ta haifarwa ‘yan cin walwalar jama’a a Afirka sanadiyar yaki da kwararar bakin haure.

Amandine na mai cewa, yunkurin hana wa bakin haure ratsa Libya domin shiga Turai wani shiri ne da a fili ake gane cewa, ya sabawa dokokin ‘yan cin dan adam, wanda kuma a zahiri babu kanshin gaskiya a game da barazanar mamayar da shuwagabanin Turai keyi.

Jin irin wadanan kalamai daga bakin wata babbar jami’ar Turai ya kara wa kungiyar AEC citoyen kwarin gwiwa a gwagwarmayar da ta sa gaba, don kawo karshen cin zarafin ‘yan ci rani, injin wani kusanta, KakaTouda.

Yaki da kwarar bakin haure zuwa turai wata hanya ce da ke samar da kudaden shiga wa wasu shuwagananin nafiyar Afirka saboda haka shugaban kungiyar JIMED mai kare hakkin bakin haure, malan Nabara Hamidou, ke ganin akwai bukatar fadakar da irin wadanan shuwagabanin illar wannan dabi’a..

Ga dai wakilinmu Sule Barma da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Shagulgulan Tunawa Da Bakin Haure Ta Duniya A Jamhuriyyar Niger 03'03"