Harin Madagali: Gwamnatin Jahar Adamawa Za Ta Taimaka

  • Ibrahim Garba

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Madagali

Da alamar an fara kai dauki ga wadanda harin da aka kai Madagali ya rutsa da su.

A yanzu adadin wadanda su ka rasu a madagali, jahar Adamawa ya zarce 30 da aka kiyasta tun farko, a daidai lokacin da gwamnatin jahar ta Adamawa, ta bakin gwamnatin jahar, ke alkawarin daukar nauyin jinyar wadanda abin ya rutsa da su.

Da yak e jawabi ga manema labarai, gwamna Muhammad Bindow Jibrilla, y a yi kira ga jama’a da su zamanto masu kula ganin yadda ‘yan Boko Haram ke ta bullo da dabaru iri iri na kai munanan hare hare. To amma ya ce ya na da kwarin gwiwar cewa ba da dadewa ba za a yi galaba kan yan Boko Haram.

A halin da ake ciki kuma, jama’a na bayyana gamsuwarsu da yanke shawarar da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yanke ta daukar ‘yan bangar da su ka nuna bajinta aikin soji. Hasali ma, shugaban kungiyar ‘yan banga a jahar, Alhaji Bako Ali, y ace wannan matakin zai yi matukar kara masu kwarin gwiwa.

Ga wakilinmu na jahar ta Adamawa da cikakken labarin:

Your browser doesn’t support HTML5

Harin Madagali: Gwamnatin Jahar Adamawa Za Ta Taimaka-4'06''