Hotunan Isar Shugabannin Duniya Babban Taron G20 a Jamus

Isowar Shugaban kasar Amurka Donald Trump a birnin Hamburg dake Jamus, ranar Alhamis 6 ga watan Yuli shekarar 2017.


 

Isowar Firai ministan Canada Justin Trudeau tare da dansa Hadrien da kuma uwargidansa Sophie Grégoire-Trudeau a birnin Hambourg dake Kasar Jamus, ranar Alhamis 6 ga watan Yuli shekarar 2017.

 

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma tare da uwargidansa Thobeka Madiba Zuma a lokacin isowarsu birnin Hamburg dake kasar Jamus, ranar Alhamis 6 ga watan Yuli shekarar 2017.

 


Shugaban kasar Argentina Mauricio Macri tare da uwargidansa Juliana Awada a lokacin isowarsu filin jirgin saman birnin Hamburg don halartar taron G20 a kasar Jamus, ranar 6 ga watan Yuli na shekarar 2017.

 

Shugaban China Xi Jinping tare da uwargidansa Peng Liyuan a lokacin da suka sauka a jirgi a birnin Hamburg dake kasar Jamus, ranar Alhamis 6 ga watan Yuli shekarar 2017.


.

Isowar Shugaban Korea ta Kudu, Moon Jae-in tare da uwargidansa, Kim Jung-sook a birnin Hamburg dake Jamus, rånar Alhamis 6 ga watan Yuli na shekarar 2017.