Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Ya Isa Birnin Paris


Bayan ganawa da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron, shugaba Donald Trump zai kuma halarci bikin Ranar Kasa a birnin na Paris.

Shugaban Amurka Donald Trump ya isa birnin Paris yau Alhamis don tattaunawa akan yaki da ta’addanci da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, don kuma ya halarci bukin ranar hutun kasa a Faransa, da ake kira Bastille day a turance, hade da kuma bukin cika shekaru 100 da dakarun Amurka suka shiga yakin duniya na daya.

Shekara daya da ta gabata, Trump ya bayyana birnin Paris a matsayin “mummunan wuri mai cike da hargitsi saboda ‘yan ta’addan da ke gudanar da ayyukansu a can. Kwanan nan ma sai da ya ce hare-haren ‘yan ISIS a Paris din sun ragewa birnin kima a idon duniya.

Yayin da shugaba Trump ya fidda Amurka daga yarjejeniyar kasa-da-kasa da aka cimma a birnin Paris a shekarar 2015, ta magance gurbatacciyar iska, shugaban ya ce an zabe shi ne don ya wakilci Pittsburg, ba Paris ba.

Duk da haka, daga baya Trump ya karbi goron gayyatar Macron zuwa wadannan bukukuwan na Faransa da ake gudanarwa a yanzu.

Bayan ganawa da Macron yau Alhamis, Trump zai yi liyafa da jami’an rundunar sojan Amurka zai kuma kai ziyara kabarin Napoleon Bonaparte.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG