Hukumar dake Kula da Saka Hannun Jari a Najeriya Ta Gina Wata Makarantar Firamare a Jihar Borno

Makarantar da Nigeria Stock Exchange ta gina a Maiduguri, Borno

A matsayin tata gudummawar, Cibiyar Hannayen Jari ta Najeriya (Stock Exchange), ta mikawa gwamnatin jihar Borno makarantar firamaren da ta gina a anguwar Bulunkutu, anguwar da ta dade tana kukan a gina mata makaranta

Cibiyar Hannayen Jari ta Najeriya, watau Stock Exchange, ta mikawa gwamnatin jihar Borno wata makarantar firamaren da ta gina a anguwar Bulunkutu cikin Maiduguri.

An gina makarantar ne a anguwar domin ba ‘ya’yansu damar samun ilmi saboda mutanen wurin sun dade suna kukan a gina masu makaranta.

Gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya yabawa hukumar da ta gina makarantar tare da kiran masu hannu da shuni su taimakawa jihar wacce kungiyar Boko Haram ta rugurguza harkokinnta na ilmi ko ina a cikin ihar.

Oscar Onyemade, shugaban hukumar, yace fahimtar cewa fannin ilmi ne da zasu iya taimakawa sosai¸yasa suka gina makarantar mai azuzuwa tara, wacce kuma aka gina a kan kudi sama da Naira miliyan 50.

Ga rahohoton Haruna Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar dake Kula da Saka Hannun Jari a Najeriya Ta Gina Wata Makarantar Firamare a Jihar Borno - 3' 17"