Hukumar DPR Ta Rufe Wasu Gidajen Mai Na Bugi

Yayin ziyarar ba zata da jami’an hukumar kula da albarkatun man fetur ta DPR, hukumar ta bankado wasu gidajen mai dake fasa kwabrin man fetur zuwa ketare, da wasu gidajen mai da ke tsuke bututun sayar da mai.

Gidajen mai shida ne dai suka fada tarkon hukumar ta DPR, a kananan hukumomin Gombi, Hong, Mubi ta arewa da kuma Mubi ta Kudu.

Babban jami’in hukumar wato Operations kwanturola, mai kula da jihar Adamawa Alhaji Ibrahim Ciroma, shine ya jagoranci wannan samamen.

Inda yace wannan abun takaici ne, kuma mun sha gargadin masu gidajen man, yanzu haka mun gano akwai kusan gidajen mai 45 da basu da rajista a jihar ta Adamawa.

Kuma tuni har an mika sunayen su ga rundunan 'yan sandan jihar domin daukan mataki, ya kara da cewar zasu ci gaba da wannan aiki ba sani ba sabo Alh. Ibrahim Ciroma.

Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN, ta nisan ta kanta daga wadannan gidajen man da ake zargi, tace ba 'ya'yan kungiyarta bane.

Alh. Abubakar A. Butu, wanda shine shugaban kungiyar dillalan man, da ke kula da jihohin Adamawa da Taraba yayi wannan karin hasken.

Ga rahoton da Ibrahim Abdul'aziz ya hada muna.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar DPR Ta Rufe Wasu Gidajen Mai Na Bugi 3'20"