Hukumar habaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, Ta Kuduri Aniyar Hana Barace-Barace a Yankin

Shugabannin ECOWAS

[Hukumar habaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka na ganin lokaci ya yi da za’a haramta yin barace-barace a cikin kasashen tare da karkata akalar masu baran kan hanyoyin dogaro ga kai

Duk da cewa babu wasu alkalumman dake fayce adadin mabarata a kasashen yammacin Afirka, Hukumar ta ECOWAS tana ganin lokaci ya yi da za’a haramta barace barace domin a dora almajirran akan hanyar neman na kai ta hanyar sana’a.

‘Yar Majalisar Dokoki, Halima Mamman mai wakiltar Jumhuriyar Nijar, ta ce idan aka duba kasashen Inyamurai ko Benin babu mai bara sai dai a same su a cikin ‘yan arewacin Najeriya da kasar Nijar. Tace ko addini da yace a yi bara, ya jadadda a yi ne daidai abin da mutum zai ci. kuma da zara ya samu kamata ya yi ya koma gida. Amma yanzu wasu sun maida ita sana’ar tara dukiya.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar dake Kula da Saka Hannun Jari a Najeriya Ta Gina Wata Makarantar Firamare a Jihar Borno - 3' 17"