Hukumar Kwastam Ta Najeriya Tayi Wani Babban Kamu

Hukumar Kwastam ta jihar Ogun, ta kama wasu manya manyan motoci cike da Katakwaye, wasu cike da naman Talo Talo dama wasu goma cike da buhuhuwan shinkafa, a bakin iyakar Najeriya da kasar jamhuriyar Benin.

Sabon shugaban hukumar kwastam mai kula da jihar Ogun, Mr Waindu Multafu, ya tabbatarwa Muryar Amurka faruwar wannan kamu, da cewa ana kokarin fita da shigar wadannan kayayyaki ne ba tare da iziniba musammam ma yadda ake kokarin fita da katakwaye wanda aka haramta fitar da su daga Najeriya.

har yanzu dai ba’a kiyasta jimlar kudaden kayayyakin da aka kama ba. wasu daga cikin direbobin motocin sun gudu haka kuma mutanen da aka kama ba ‘yan Najeriya bane kuma majiya yaren Faransanci kawai.

Mr. Multafu yayi kira ga ‘yan kasuwa da su rika bin dokoki wajen gudanar da kasuwancin su a ko ina, idan kuwa basu bi ba to hukumar kwastam a shirye take ta kwace duk kayan da ta kama tare da hukunta duk wanda aka kama.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwastam Ta Najeriya Tayi Wani Babban Kamu - 2'41"