Hukumar MDD dake Kula da 'Yan Gudun Hijra a Nijar Na Fuskantar Karancin Kudi

Tawagar UNHCR a Nijar

Wasu kasashen duniya basu cika alkawarin da suka yiwa UNHCR, hukumar Majlisar Dinkin Duniya dake kula da 'yan gudun hijira a Nijar ba lamarin da ya sa ta fuskanci karancin kudi kuma bata iya kula da 'yan gudun hijiran dake Nijar ba, wadanda suka fito daga kasashe uku

'Yan Najeriya da suka tserewa rikicin Boko Haram wajen 200,000 ne ke gudun hijira a yankin Diffa.

Baicin 'yan Najeriya dubban 'yan kasar Nijar ne rikicin ya tilasta masu gujewa daga garuruwansu na asali suka bazu a wurare daban daban.

Akwai kuma 'yan kasar Mali da su ma suna gudun hijira a yankin Tilaberi da Tawa a sanadiyar mamayar da 'yan ta'adda suka yiwa arewacin kasar kamar yadda hukumar UNHCR ta sanar.

Hukumar ta yaba da hukumomin Nijar da yadda mutanen kasar ke zaune lafiya da 'yan gudun hijiran.

Amma a bayanan da suka bayar a karshen ziyarsu zuwa kasar Nijar, manzo na musamman na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ko MDD mai kula da 'yan gudun hijira da daraktan UNHCR a nahiyar Afirka sun nuna damuwa akan rashin wadatattun kudaden da zasu dauki dawainiyar 'yan gudun hijiran.

A cewar wadannan shugabannin a cikin dala miliyan tamanin da shida da suke bukata domin ayyukan tallafawa 'yan gudun hijira a Nijar a wannan shekarar 2017 miliyan 34 kacal ne suka shigo. Saboda haka suna kiran masu hannu da shuni su agaza.

Ga karin bayani daga rahoton Souley Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar MDD dake Kula da 'Yan Gudun Hijra a Nijar Na Fuskantar Karancin Kudi - 2' 50"