Hukumar NNPC Ta Wadata Najeriya Da Man-Fetur - Kyari

Malam Mele Kyari

Matsalar karancin man fetur zata zama tarihi a Najeriya nan bada jimawa ba, a cewar Shugaban Kamfanin NNPC, Alhaji Mele Kyari.

Tun bayan barkewar zanga-zangar kawo karshen rundunar 'yan sanda ta SARS, Najeriya ta fuskanci matsaloli daban-daban, kama daga sace-sace, cin zarafin al'umma zuwa karancin man fetur da ake fama da shi a wasu yankunan kasar.

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Alhaji Mele Kyari, ya yi bayani a kan yanayin da a ka shiga na karancin man fetur a wasu sassan Najeriya. Ya ce nan bada jimawa ba, za a kawo karshen wanna matsalar.

Matsalar ta samo asali ne daga rashin samun damar kai mai daga kudancin kasar zuwa arewaci, saboda tsoron tarzoma da direbobin ke yi. Kasar na da mai fiye da adadin da take bukata don amfanin 'yan kasa, karancin shi bashi da alaka da rashin shi.

ABUJA: NNPC

Wani direban tankin mai mai suna, Alhaji Nkurna, ya yi bayani ana su bangaren na direbobi motocin mai akan yanayin da suka tsinci kansu a kan hanyar dakon mai zuwa Abuja.

Ya ce sun dakatar da tafiye-tafiye don gudun masu zanga-zanga, wanda suke ganin ana iya kona motocinsu, sun makale a cikin daji ba abinci, don haka suna neman mahukunta su dauki matakan da suka dace cikin gaggawa.

Ma’aikaci a wani gidan mai, Ibrahim Habib Sarino ma ya yi bayani a kan fara samun sauki a lamarin karancin man fetur a Abuja.

Shi ma tsohon shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta wato IPMAN Alh. Musa Muhammad Felande, yace babban fatansu shine a kawo karshen safarar mai ta manyan tituna a kasar.

An dai fara fuskantar karancin man fetur a babban birnin tarayyar Najeriya da birane makwabta ne tun karshen makon da ya gabata inda wasu ‘yan kasar ma suka dora alhakin ga zanga-zangar EndSars.

Ga rahoton Halima Abdulra’uf a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar NNPC Ta Wadatar Da Kasa Da Man-Fetur- Kyari