Hukumar Raya Dimokradiya Ta Amurka Ta Shiryawa Majalisar Dokokin Nijar Fadakarwa Akan Ma'adanai

Taron fadakarwa akan dokokin ma'adanai

Lura da wasu kurakurai da bincike ya gano a cikin dokokin kasar Nijar idan aka kwatantasu da dokokin kasa da kasa a fannin ma'adanai ya sa hukumar raya dimokradiya ta kasar Amurka shiryawa majalisar dokokin Nijar taron fadakar domin su gane rawar da yakamata su taka wajen daidaita dokokin Nijar da na kasa da kasa

Wakilin hukumar raya dimokradiya ta Amurka yace taron na gudana ne a washegarin da wasu 'yan majalisar kasar ta Nijar suka ziyarci wuraren da ake hakan zinariya da kuma inda ake tace man fetur domin ganin yadda ayyuka ke gudana.

Taro akan dokokin ma'adanai

Onarebul Yahaya Jibrin yace da a ce ana samu ana zama a tattauna da an ciwo kan wasu abubuwan dake faruwa. Yace inda ake hakar zinariya kowace shekara ana fitar da kudi kimanin miliyan dari na sefa domin inganta kayan jin dadin jama'a, amma ba haka lamarin yake ba. Baicin hakan, akwai wasu abubuwa da ake tilastawa mutane suyi wadanda kuma basa cikin tsarin dokoki. Yace zasu zauna su tattauna akansu.

Shigar da wasu mahimman ka'idodin dake da nasaba da 'yancin dan Adam tare da zuba ido akan yadda hakan ma'adanai ke gudana domin tantancewa idan ana mutunta doka ko a'a na cikin abubuwan da aka bukaci 'yan majalisan dake halartar taron su maida hankali a kansu.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Raya Dimokradiya Ta Amurka Ta Shiryawa Majalisar Dokokin Nijar Fadakarwa Akan Ma'adanai - 3' 25"