Hukumar USAID Ta Kuduri Aniyar Tallafawa Wasu Jihohin Nijar

Hukumar USAID A Taron Tallafawa Wasu Jihohin Nijar

A jamhuriyar Nijar hukumar raya kasashe ta Amurka da ake kira USAID a takaice ta kaddamar da wani shiri na musamman da nufin tallafawa al’umomin jihohin Maradi da Zinder, wanda zai maida hankali wajen samar da wadatar abinci, ruwan sha, da yaki da cutar Tamoa, da kuma kyautata sha’anin kiwon lafiya a tsawon shekaru 5.

Hukumar USAID A Taron Tallafawa Wasu Jihohin Nijar

Kimanin biliyan 90 na CFA ne hukumar ta USAID ta yi alkawarin kashewa a karkashin wannan shirin da ake kira Food for Peace, wanda zai shafi miliyoyin mutanen jihohin biyu.

Gwamnonin jihohin da za su ci moriyar wannan shirin sun yaba da yunkurin na USAID.

Hukumar USAID A Taron Tallafawa Wasu Jihohin Nijar

"Wannan shirin zai samar da sauyin rayuwa ga talakawan karkara da matsalar ta fi shafa," a cewar gwamnan jihar Maradi Zakari Oumarou.

Kungiyoyin agajin da su ka hada da Save The Children, da CRS, da kuma CARE ne hukumar ta USAID ta baiwa amanar gudanar da wadannan ayyukan, da hadin guiwar wasu kungiyoyin cikin gida.

Wannan wani bangare ne na ayyukan da hukumar USAID ke gudanarwa kai tsaye shekaru kusan 40 kenan a fannonin da suka shafi talakawa a wannan kasa.

A saurari rahoto cikin sauti daga Nijar.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar USAID Ta Kuduri Aniyar Tallafawa Wasu Jihohin Nijar