Hukumar Zaben Najeriya (INEC) Tace Za'a Sanarda Sakamako a Kowace Mazaba

INEC

A wannan zaben me zuwa hukumar zabe me zaman kanta, tace za'a bayyanar da sakamakon zabe a kowace mazaba.

Hukumar zaben me zaman kanta ta Najeriya wato INEC tace a shirye take don gudanar da zabe nan da kwanaki talatin da biyu (32). A cewar jami’in yada labarai na hukumar Mr. Nick Dazan, yace wannan karon sun dauki kwararan matakai don ganin an magance duk wasu matsaloli na almundahanar zabe.

Yayi nuni da cewar a wannan karon sun fito da wani tsari wanda kowace mazaba zatasamu kalar katin kada kuri’ar sirin ta da ban da na makociyar ta, wanda zai banbanta kowace mazaba. Yace ko wane katin sirri na kada kuri'a yanada wata lamba wadda babu irinta don tabtabcewa.

Kana kuma kowane akwatin zabe na da lamba ta mussaman, wanda baza’a iya dauka don kaiwa wata mazaba ba. Wani babban mashahurin shirin shine a wannan karon za’a sanar da sakamakon zabe na duk ilahirin cibiyoyin zabe dubu dari da ashirin (120,000) a kowace mazaba, don haka mutane zasu iya tsayawa don ganin sakamako a nan take kuma za’a manna wannan sakamakon a nan wajen kamin a wuce da sakamakon zuwa mattatrar sakamako a karamar hukuma, kana zuwa jiha sannan tarayya.

Ya kara da cewar suna kira ga duk ‘yan takara da su tabbatar sun sa wakilansu amintattu don gujema sayansu. Yace wannan katin zabe na din-din-din da akaba wa kowane me zabe yana dauke da abubuwan sirri wanda kwamfutar su kadai zata iya gani, tayyada wani bazai iya amfani da nawani ba, domin idan aka sa wanna katin zai nuna hoton mutun da adireshin shi da kuma inkiyar mutun da hoton zannen hannunshi.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakamakon zabe a Mazaba - 2'39"