Hukumar Zaben Najeriya Ta Sake Bude Kofar Mika Sunayen 'Yan Takara

INEC

Hukumar zaben Najeriya tace har yanzu kofa tana bude na shigar da sunayen 'yan takara,a kamar yadda aka yayata tun farko ba.

Kakakin hukumar Aliyu Bello ya ce akwai fiye da mako daya nan gaba ma tura sunayen ‘yan takarar da su ka shafi taraiya.

Hakan zai zama labari mai dadi ga ‘yan takarar da suka kawo korafi musamman ga jam’iyyar APC cewa sun lashe zaben fidda gwani amma aka tura sunayen wasu ‘yan lele.

Daga cikin wadannan suka mika irin wannan korafin akwai Usman Tugga da ya nemi takarar dan majalisar dattawa daga Bauchi wanda ya mika korafi ga uwar jam’iyyar APC na nuna an ma sa durmukel.

Hakanan Komred Murtala Garba daga Taraba ma da ya nemi takarar majalisar wakilai daga yankin Takum da Donga ya kawo korafin.

Korafe-korafen sun hada da na ‘yan takarar gwamnoni a kusan duk sassan Najeriya da ke neman a soke zaben da aka gudanar ko a musanya sunayen wadanda su ka ce rubutawa kawai a ka yi.

APC dai ta nada tsohon gwamnan Edo Farfesa Osunbor don jagorantar kwamitin karbar korafin da samar da maslaha.

Saurari Rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

Your browser doesn’t support HTML5

Mika Sunayen 'yan takara ga INEC-3:30"