Hukumomin China Na Amfani Da Wata Manhaja Wajen Binciken Musulman Kasar

Hukumomin kasar China na amfani da wata babbar manhaja wajen gano Musulmai, da yin bincike akan su, da kuma tsare su a arewa maso yammacin yankin Xinjiang, a cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights watch da ake kira HRW a takaice.

Kungiyar da mazaunin ta ke birnin New York, ta fada yau 2 ga watan Mayu cewa, hukumomin na amfani da wannan manhajar wajen samun bayanai daban-daban masu yawa daga jama’ar Xinjiang, kama daga rukunin hallitar jininsu, da tsayinsu, da kuma al’amuran addininsu da na siyasa.

Manhajar na kuma sa ido akan kai da komon jama’a ta hanyar yin amfani da wayoyin hannunsu, da motocinsu, da katin shedar zama dan kasarsu, ta na kuma daukar bayanan wasu dabi’u da ba ta gane masu ba, kamar ko mutum baya hulda da makwabtansa ko yana amfani da wutar lantarki fiye da kima a cewar kungiyar ta HRW.

‘Yan sanda a Xinjiang na amfani da bayanan da aka samo ba bisa ka’ida ba akan gaba dayan dabi’un jama’a na doka, suna kuma yin amfani da su don su muzguna masu , a cewar Maya Wang, babbar mai binciken kungiyar HRW a China.

Sai dai hukumomin China sun sha musanta wadannan zarge-zargen.