Imo: An Ceto Wasu Mazauna Amurka Daga Masu Garkuwa

Malam Dasuki Galadanchi

Dubun wasu masu garguwa da mutane don a ba su kudin fansa ta cika, bayan da 'yan sandan jahar Imo su ka damko su a daidai lokacin da su ke kan shagali da wani kudin fansa na dalolin Amurka.

Yayin da ake ci gaba da kokarin inganta lamuran tsaro a duk fadin jihar Imo, ita ko rundunar ‘yan sandan jihar ta ce, a halin yanzu, ta kwato wani mutum da matarsa mazauna Amurka daga hannun masu garkuwa da mutane.

Malam Dasuki Galadanchi, kwamishinan ‘yan sandan a jihar, ya yi karin haske akan lamarin inda ya ke cewa sun samu nasarar kama mutanen ne biyo bayan yadda suke ta kashe-kashen kudaden kasar waje, wanda shi ya ja hankalin jama'a.

Daga karshe dai, kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bada goyon baya a kokarin da ake yi na murkushe miyagun laifuka, da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar baki daya.

Ga dai wakilinmu Alphonsus Okoroigwe da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Imo: An Ceto Wasu Mazaunan Amurka Daga Masu Garkuwa 2'10"