Ina Aka Kwana Kan Batun Kasafin Kudin Badi Da Buhari Ya Gabatar?

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Majalisar ta kama hanyan cika ka'idar kasafin kudin Janairu zuwa Disamba domin kara azama na daidaito ga tattalin arzikin kasa.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ne ya bayyana hakan inda ya ce kawai abin da ya rage shi ne alkawali da shugaban kasa ya yi na cewa za a sake sakin kudin domin a ci gaba da ayyuka.

Ya kara da cewa, yanzu majalisa za ta ci gaba da yi wa kwamitin kasafi bayani kafin a kai kundin ga Shugaban kasa ya sa hannu kafin watan Disambar na bana.

Kasafin na bana dai na Naira Triliyan 10.7 wanda ya zama kasafi mafi tsoka da shugaba Buhari ya taba yi amma kuma ya ba da umurnin cewa ba za a yi sabbin ayyuka ba.

Sai dai Sanata Yusuf Abubakar Yusuf ya yi wa kalaman na Buhari fashin baki, inda ya ce dole ne a kashe kudi daga cikin sabon kasafin na yin wasu muhimman ayyuka ko dan yaya ne.

Yusuf ya kara da cewa ai rashin daidaita lokacin sakin kasafin ne ya ja haka amma a wannan tun da an kama hanyan kammala shi komi zai daidaita.

Daya cikin shugabanin adawa a Majalisar Sahabi Ya'u, ya ce in har batun cewa ko sun gamsu da kasafin abu ne mai wuya amma dai sun kula cewa Shugaba BuhariI ya yi kokari wajen amfani da abin da kasar ke da shi ne domin a yi wa al'umma ayyuka.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda domin jin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Ina Aka Kwana Kan Batun Kasafin Kudin Badi Da Buhari Ya Gabatar? - 3'31"