Yanzu kasar Indiya ta zarce kasar Brazil a matsayin kasa ta biyu a duniya a yawan masu dauke da cutar corona.
WASHINGTON D.C. —
Yau Litinin Ma’aikatar lafiyar kasar ta Inidya ta ba da rahoton samun sabbin kamuwa da cutar wajen 90,802.
Hakan ya sa adadin masu dauke da cutar a kasar ya karu zuwa sama da miliyan 4.2 tun bayan barkewar cutar.
Ta kuma samu karin adadin mace-mace na 1,016, wanda ya sa adadin wadanda cutar ta kashe a kasar ya kai 71,642.
Kasar Brazil ta bada rahoton samun sabbin kamuwa 14,521 jiya Lahadi, amma a yayin da a yanzu ta ke bayan Indiya a yawan masu dauke da cutar, har yanzu ita ce ta biyu bayan Amurka a yawan wadanda su ka mutu, inda ta ke da 126,650.
Amurka na kan gaba da yawan masu dauke da cutar miliyan 6.3 da kuma wadanda su ka mutu 189,000.