INDONESIA: Mutun Uku Sun Mutu A Harin Ta'addanci

Harin taaddanci a Indonesia

A Indonesia anji karar wasu fashe fashe masu yawa sannan daga bisani aka ji amon bindiga a Jakarta babban birnin kasar jiya Alhamis.

Akalla mutane uku sun mutu, kamar yadda shaidun gani da ido suka yi bayani.
Kafofin yada labaran kasar suka ce anji fashe fashe daban daban har shida a tsakiyar birnin, kusa da kasuwar zamani da ake kira Sarinah. Haka nan akwai ofisoshin gwamnati da kuma manyan O'tel O'tel a unguwar.

'Yansanda suka wasu daga cikin fashe fashen bama-bamai ne suka haddasa su. Babu tabbas kan wadanda suka kai harin, ko an kama wasu daga cikin maharan.