Iran: Amurka Bata Da Aikin Yi, Sai Wasan Yara

A yau Talata hukumomin kasar Iran sunyi watsi da matakin da Amurka ta dauka na kakaba mata takunkumi, don kawo karshen takun saka da ake tsakanin kasashen biyu. Iran din dai ta ayyana kiran na Amurka don sasantawa a matsayin wasan yara.

A jiya Litinin dai shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu akan wani shirin kakaba takunkumin tattalin arziki ga shugaban kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, tare da wasu jiga-jigain hafsoshi 8 na rundunar sojojin kasar.

Trump ya nemi Gwamnatin Iran ta sauya halayenta, ta mutunta bil’adama, kuma ta dawo kan taburin sulhu don warware matsalolin da take fuskanta.

Mai baiwa shugaban kasar shawara a harkar tsaro John Bolton, a wata ziyara da ya kai yau a birnin Kudus, ya bayyana cewa kofar shugaba Trump a bude take don tattaunawa, amma Iran din ta ki amsa tayin na a sasanta.