Italiya Ta Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Azabtar Da Bakin Haure

Lokacin da ake sauke wasu bakin haure a tashar jiragen ruwa ta Pozzallo a Italiya

Yan sandan Italiya sun cafke wasu mutane uku wadanda ake zargi da karbar kudade da azabtar da bakin hauren a cibiyar da ake tsare da su a Libya.

Masu gabatar da karar sun ba da umurnin a kama wasu ‘yan kasar Masar su biyu da wani dan kasar Guinea, bayan da bakin hauren da dama suka gane su a matsayin wadanda suka azabtar da su.

Ana zargin mutanen da kafa wani matsuguni a wani tsohon sansanin soji da ke Libya.

“An sha duka na a sansanin. Na fuskanaci ukuba sosai har na samu tabo a jiki na,” Inji daya daga cikin bakin hauren yayin da yake ganawa da masu gabatar da karar.

Wasu daga cikin bakin hauren sun yi zargin an yi wa mata fyade sannan an kashe mutanen da suka kasa biyan kudin fansa, ko kuma aka sayar da su ga masu safarar mutane.

Gungun- gungun tsageru ne ke rike sansanonin bakin haure a Libya, inda a nan ake ajiye su idan sun isa kasar a yunkurin da suke yi na kai wa ga nahiyar turai.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama, sun sha kira ga gwamnatin kasar ta Libya da ta rufe wadannan sansanoni na bakin haure, saboda a cewarsu wurare ne da ake azabtar da jama’a.