Jam'iyyar PNDS ta Tsaida Bazoum Mohammed a Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

A jamhuriyar Nijer kwamitin zartarwar jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki ya bayyana sunan shugaban jam’iyyar na kasa Bazoum Mohamed a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2021 da za a yi a kasar, duk kuwa da cewa akwai jita jitar fuskantar rarrabuwar kawuna a tsakanin jiga-jigan jam’iyyar dangane da maganar wanda ya cancanci a baiwa wannan tikiti.

A yayin zaman su na jiya Lahadi ne mambobin kwamitin zartarwar jam’iyyar PNDS tarayya mai mulki suka yanke shawarar zaben Bazoum Mohamed a matsayin gwarzon su na zaben shugaban kasa na shekarar 2021 a karkashin tutar wannan jam’iyya wace a baya-bayan nan ake yada jita-jitar cewa sakataren ta Hassoumi Massaoudou yana sha’awar samun wannan tikiti. Abinda wasu ke ganin sa a matsayin musabbabin korarsa daga mukamin ministan kudin Nijer.

Hon. Idrissa Maidaji, dan majalisar dokokin kasa ne a karkashin inuwar jam’iyyar PNDS ya tabbatar da cewa a babban taron jam’iyyar ne aka amince da Mohammed Bazoum a matsayin dan takarar jam’iyyar PNDS.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyyar PNDS ta Tsaida Bazoum Mohammed a Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa - 2'45"