Jam'iyyun Siyasa Sun Nemi Jama'a Su Mutunta Hukuncin Kotun Koli

A Najeriya, yayin da babbar kotun koli ta kasar ta ayyana gobe Litinin a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin kararrakin zabe na wasu gwamnonin jihohi da aka gabatar mata, a gefe guda kuma jam’iyyun siyasa sun yi kira ga magoya bayansu da su kaurace wa duk wani abun da zai kawo tashin-tashina a dangane da irin hukuncin da kotun kolin za ta bayyana.

A Jihar Bauchi, akwai shari’a tsakanin jam’iyyar PDP da kuma jam’iyyar APC wadda ta ke kalubalantar nasarar lashe zaben da jam’iyyar PDPta yi a zaben shekarar bara. A dangane da hakan jigo a jam’iyar APC ya shawarci magoya bayansu da su kasance masu bin doka da kuma umurnin kotu.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Bauchi shi ma ya bukaci zaman lafiya a dangane da irin sakamakon da zai bayyana.

Gamayyar kungiyoyin farar hula ta gudanar da taro a sakatariyar ‘yan jarida a Bauchi, domin yin kira ga matasa da kuma ‘yan siyasa, dangane da muhimmancin zaman lafiya.

Saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam’iyun Siyasa Sun Yi Kira Ga Magoya Bayansu Da Bin Umurnin Kotu