Jama'a Sun Bayyana Ra'ayoyinsu Kan Yadda Za A Shawo Kan Matsalolin Tsaro

Muryar Amurka ta gudanar da taro na samo bakin zaren warware matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya a garin Maiduguri
Jama'a da suka halarci taron da Muryar Amurka ta shirya kan yadda za a iya shawo kan matsalolin tsaro, sun bayyana ra'ayoyi dabam-dabam kan yadda za a iya cimma wannan.

A wajen wannan taron da aka gudanar a garin Maiduguri, jama'a sun yi tattaki daga sassa da dama na Jihar Borno da kuma makwabciyarta Jihar Yobe, inda suka zo da guri guda daya: watau yadda zasu iya bada gudumawa wajen kawo karshen wannan matsala da ta addabi yankin musamman.

Wakilin sashen Hausa, Haruna Dauda Biu, ya hada rahoto na musamman na ra'ayoyin wadannan jama'a.

Your browser doesn’t support HTML5

Tattaunawa da Al'umma Kan Tsaro A Maiduguri, Jihar Borno - 2:43