Jam'iyyar APC Ta Yi Allah Wadarai Da Kalamun Labaran Maku

Atiku Abubakar

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC mai kula da Arewa maso Gabas, Dr. Umar Duhu, yace kalamun ministan neman haddasa fitina a cikin kasa ce.
Jam'iyyar APC ta yi Allah wadarai da kakkausar harshe da kalamun ministan yada labaran Najeriya, Labaran Maku, wanda ya bayyana Atiku Abubakar da gwamnonin da suka bar jam'iyyar PDP suka koma APC a zaman "Fulani Makiyaya" wadanda ba su iya zama wuri guda.

Da yake ganawa da 'yan jarida a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa mai kula da yankin arewa maso gabas, Dr. Umar Duhu, yace kalamun na Labaran Maku na haddasa fitina a cikin kasa ne, kuma na nuna kyamar wata al'umma.

Shi dai tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ki yarda ya mayarda martani kai tsaye ga kalamun na Labaran Maku, amma kuma yayi watsi da jam'iyyar PDP yana mai kira ga dukkan magoya bayansa da su je su yi rajista a cikin jam'iyyar APC.

Turakin na Adamawa yace jam'iyyar APC ita ce zata iya samar da sauyi na zahiri a cikin kasar.

Masu fashin baki da dama su ma sun ja kunnen 'yan siyasa da suyi taka tsantsan wajen kalamunsu domin gudun janyo wata fitina a yayin da zabe ke kara kusantowa.

Your browser doesn’t support HTML5

APC Ta Yi Tur Da Kalamun Labaran Maku - 3'08"