Jamhuriyar Niger tana samun nasara akan Boko Haram

'Yan gudun hijira

Baban kwamdan sojoji jamhiruyar Niger Janaral Seini Garba yace sojoji suna samun nasara a fafatawar da su ke yi da yan Boko Haram a yankin Diffa.

Jamhuriyar Niger ta baiyana samun nasara sosai a yakin da take fafatawa da yan kungiyar Boko Haram a yankin Diffa dake makwaptaka da jihohin Yobe da Borno arewa maso gabashin Nigeria.

Baban kwamandan rundunar mayakan kasar Janaral Seini Garba ne ya baiyana haka, a lokacinda yake hira da manema labaru a wurin bikin gabatar da sakon barka da shiga sabuwar shekara ga shugaban kasar Niger Isoufou Maahammadou.

Shugaban jamhuriyar Niger

Janaral Garba ya baiyana cewa su dauki tsauraran matakai a saboda haka suna samun kyakyawar sakmako a fafatawar da su ke yi da 'yan Boko Haram.

Yace suna tsamani sun fara samun galaba a wannan yaki. Kodayake da sauran rina a kaba, domin har yanzu kungiyar ta Boko Haram tana barazana ga zaman lafiya, saboda miyagun makaman data mallaka.

Yace kasar Niger ta dandana kudarta a shekarar data gabata a sakamakon hare haren da Boko Haram ta kaddamar a yankin Diffa, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, yawancin su fara hula.

Dubban jama'ar yankin Diffa ne suka arcewa rikicin Boko Haram, kodayake wasu bayanai sun ce an fara samun mutanen da suka fara komawa garuruwan su.

Your browser doesn’t support HTML5

Sanarwar baban hafsan sojojin jamhuriyar Niger 1'30"