A yau Asabar jami’an Afghanistan suka sanar da cewa jami’an tsaro sun sake kwato wata muhimmiyar gunduma a arewa maso gabashin kasar daga hannun ‘yan Taliban bayan shekaru 5, a yayinda ake ci gaba da gwabza kazamin fada a wasu lardunan Afghanistan.
Kungiyar Taliban ta kara zafafa hare-haren ta duk da cewa wakilan kungiyar sun sake hawa kan teburin shawarwari da Amurka a Qatar don kawo karshen yakin na Afghanistan wanda aka kwashe shekaru 18 ana yi, wannan shine yaki mafi tsawo da Amurka ta shiga a wata kasar.
Ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce fadan da aka yi don kwato garin Wardoj a lardin Badakhshan yayi sanadiyar mutuwar kusan ‘yan kungiyar Taliban 100, ciki har da manyan kwamandojinsu. Ma’aikatar ta yi ikirarin cewa jami’an tsaron Afghanistan ne suka kai hare-haren ba tare da yin hasarar rai ko daya ba.
Lardin Badakhshan dai ya hada iyaka da kasashe makwabtan Afghanistan guda 3, ciki harda China, da Pakistan da kuma Tajikistan.