‘Yan Sanda A Türkiye Sun Kama Hodar Iblis Kilogram 608

Cocaine (Photo by Ludovic MARIN/AFP)

Ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiyya ya ce ‘yan sanda sun kama hodar ibilis mafi girma na uku a tarihin kasar.

WASHINGTON, D. C. - Ali Yerlikaya ya sanar a yau Alhamis cewa, an kwace kilogiram dari 608 na hodar ibilis, mafi yawanta nau’in ruwa, a wani samame da aka kai a larduna uku.

Kungiyoyin da ke sa ido kan aikata laifuka sun ce Turkiyya na bunaksa a matsayin cibiyar safarar hodar ibilis da ke shigo daga kudancin Amurka zuwa Turai.

Samamen na ‘yan sanda ya auna wani gungun ‘yan kasashen waje da ake zargin wani dan kasar Lebanon da Venezuela ke jagoranta. Ministan ya ce ana tsare da mutane 13 da ake zargi, ciki har da kasashen waje hudu.