Jami’an Jihar Sokoto Sun Ziyarci Dalibansu a Jamhuriyar Nijar

Ziyarar Jami'an Jihar Sokoto Zuwa Jami'ar Yamai

Wata tawaggar jami’an ma’aikatar ilimi ta jihar Sokoto ta ziyarci daliban jihar da ke karatu a jami’ar Yamai don duba halin da suke ciki, a ci gaba da zagayen daliban da gwamnatin sokoto ta aika kasashen waje domin neman ilimi.

Sauke nauyin da ya rataya a wuwan gwamnatin jihar Sokoto game da batun kudaden karatun dalibanta da ke jami’ar Yamai, tare da tantance zarihin halin da daliban jihar ke ciki akan yanayin rayuwa da na karatunsu, na daga cikin dalilan zuwan tawagar Yamai.

Shugaban hukumar tallafawa dalibai ta Sokoto, Altine Shehu Kajeji, ya fadawa Muryar Amurka cewa sun kai wannan ziyara ce domin ganewa idanunsu halin da daliban jihar ke ciki.

Ziyarar har ila yau ta hada har da shirin biya musu kudin makaranta dana abinci.

A cewar shugaban kungiyar daliban jihar Sokoto a Nijar, Muktar Mohammad Hassan, irin wannan ziyara wata hanya ce da ke kara musu kuzarin mayar da hankali ga karatunsu.

Ziyarar Jami'an Jihar Sokoto Zuwa Jami'ar Yamai

Tawagar masu ziyarar dai ta bayyana gamsuwa da irin kulawar da dalibai ke samu daga hukumar jami’ar Yamai, kuma a cewar jagoranta za su ci gaba da zagayen wasu kasashen na daban domin shafe hawayen daliban jihar Sokoto.

Domin karin bayani ga rahotan Sule Muminu Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami’an Jihar Sokoto Sun Ziyarci Dalibansu a Jamhuriyar Nijar- 2'53"