Jami'an kasar Libya sun dorawa magoya bayan Gadhafi alhakin hare haren bom

Libiyawa suna nuna yatsunsu bayan kada kuri'aunsu

Hukumomin kasar Libya sun ce magoya bayan hambararren shugaban kasar Moammar Gadhafi ne ke da alhakin hare haren bom biyu da aka kai kan motoci da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a Tripoli babban birnin kasar.

Bama baman biyu sun tashi ne ‘yan mintoci tsakanin juna da asubahin yau Lahadi, yayinda Libiyawa ke shirin bukin karamar sallah bayan kamala azumin watan Ramadan.

Mota ta farko tarwatse ne a babban titin birnin Tripoli kusa da kwalejin aikin soja ta yi sanadin mutuwar mutane biyu. Ta biyu kuma ta tarwatse a wani titi kusa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta yiwa mutane da dama rauni. Hukumomi sun kuma gano suka warware nakiyar da aka dana a mota ta uku a yankin.