Jami’an yaki da ta’addanci na kasashen Turai sunce ba zasuyi sakaci ba, ganin cewa duk da an kwace ikon birnin Raqqa daga mayakan kungiyar ISIS, har yanzu ‘yan ta’addaci na cikin shiri.
Murkushe kungiyar ISIS da aka yi a babban birnin Syria a farkon watannan, na nuni da yadda ake ta yayata cewa an kawo karshen kungiyar, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya fito, yana bayyana abinamatsayin babbar nasara.
Amma jami’an yaki da ta’addanci sunce akwai alamun cewa kungiyar ISIS ta yadu, musamman ma cikin wani kankanin lokaci.
Babban abin damuwa shine duk kuwa da cewa kungiyar ta rasa ikon wasu muhimman wuraren ta a Syria da Iraq, amma har yanzu kungiyar na samun yin magana da mayakanta dake Turai, da kuma samun neman sabbin mayaka.