Jam'iyyar Democrat Tayi Abun Tarihi A Amurka

Wasu mata 'yan jam'iyyar suna kukan murna, basu taba tsammanin wata babbar jam'iyya zata iya tsayar da mace ba

Hotuna 43 ne suka bayyana akan majigin filin taro inda jami’iyar Democrat take gudanar da babban taronta a Philadelphia da yammacin jiya Talata, kowane daya acikin hotunan na nuna wadanda suka zama shugabannin kasa a nan Amurka.

Bayan an bayyana hoton Shugaba Barrack Obama, sai majigin ya matso kusa ya bude wani hoto sai Hilary Clinton wacce ta zama mace ta farko da aka tsayar da ita yar takarar shugaban kasa a babbar jami’iyar Amurka


Ko shakka babu wannan dare ya kayatar kuma an yi min babban karramawa, inji Hillary Clinton.

Shugaban Amurka Barrak Obama, bakin fata na farko da ya taba zama shugaban kasa. Jam'iyyar Deocrat ta tsayar dashi


An nunata a wani bidiyo daga New York kuma tana cewa, Demokrat ta rushe katangar dake hana mata kaiwa cigaba zuwa mukamin koli a cikin aiki. Clinton tayi magana akan muhimmancin wannan rana ga kowace ya mace da take kallon wannan bidiyo


Tace tana yuwa itace mace ta farko da zata zama shugabar kasa, amma kowace daya a cikinku zata iya biyo sawu na


Babban mai jawabin goyon bayan Clinton a jiya Talata shine mijinta Bill Clinton wanda ya taba zama shugaban kasa sau biyu daga shekarar 1990 har tsawon shekaru takwas. Ya bada cikakken tarihinsu, tun lokacin haduwarsu har ya kai ga tarihin aikinta na lauya kafin ta zama Sanata sa’annan daga bisani ta zama sakatariyar harkokin wajen kasar