Janar Buratai Ya Kaddamar da Ofishin Karban Koke-koke a Barikin Maimalari dake Maiduguri

Janar Tukur Buratai cikin kayan soja tare da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya kaddamar da wasu ayyukan jin dadin sojoji da aka yi a barikin Maimalari dake Maiduguri tare da bude ofishin shigar da koke-koken jama'a

Babban Hafsan hafsoshoin sojan Nigeria, Janar Tukur Buratai, ya kaddamar da ofishin sauraren korafe korafe a barikin soja na Maimalari a Maiduguri jihar Borno.

Duk wadanda suke gannin an tauye masu hakinsu nada damar su kai kukansu a ofishin.

Baicin Ofishin karban koke koken, har ila yau babban hafsan ya kuma bude wani asibiti da aka gina tare da hadin gwuiwar kungiyar bada agaji ta Red Cross.

Haka kuma Janar Buratai ya cigaba da kaddamar da ayyukan jin dadin sojojinsa a barikin na Maimalari, ciki har da rukunin gidaje da dama.

Ga Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Janar BurataiYa Kaddamar da Ofishin Karban Koke-koke a Barikin Maimalari dake Maiduguri - 2' 51"