Jaridar New York Times Ta Yi Tonon Silili

Wata cibiyar ayyukan nukiliyar kasar Iran

Amurka na kaiwa shirin nukiliyar Iran farmaki da dabarun sadarwa na zamani

Wata babbar jaridar Amurka ta buga cewa daga kama mulki, shugaban Amurka Barack Obama ya bada umarni a asirce a yi amfani da dabarun yaki na zamani a kai hari kan fasahar kasar Iran ta sarrafa shirin ta na nukiliya ta hanayr na’urorin kwamfuta.

Jaridar New York Times ta ambaci majiyoyin da ba su so a bayyana su ba wadanda kuma suke da masaniya sosai kan shirin, sun bayyana wannan umurni da cewa babban mataki ne a fadada amfani da irin wadannan makamai masu sabbata hanyoyin sadarwa.

Akwai rahotanni dake nuna cewa tun zamanin mulkin George Bush aka fara yin amfani da shirin.

Kasashen ketare suna yin amfani da takunkumi wajen matsawa Iran lambar bin umurnin Majalisar Dinkin Duniya ta kyale Sufetocin kasa da kasa su ziyarci cibiyoyin Nukiliyar ta.

Farisa ta dage cewa shirin ta na nukiliya na yiwa farar hula ayyukan dadada rayuwa ne, amma kasashen yammacin duniya da Isra’ila su na zargin Iran da kera makaman nukiliya ne a fakaice.

Iran tana zargin kasashen yammacin duniya da Isra’ila da kai harin kan na’urorin ta na kwamfuta masu sarrafa ma ta shirin ta nukiliya.

Amma ya zuwa yanzu babu wanda ya fito ya dauki alhakin kaiwa Iran wadannan hare-hare.

Kwanan nan aka gano sabuwar hanyar da ake bi a turawa kwamfutocin Iran matsalar da jirkita mu su lissafi.