Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Ba Ta Yi Tasiri Ba A Libya

Jami’ai daga gwamnatin daya bangaren gwamnatoci biyu masu gaba da juna a Libya sun ce yaki da ya sake barkewa a jiya Lahadi, sakamakon dannawa da rundunar bangaren gabashin kasar ke yi zuwa wani yankin yammacin kasar mai muhimmanci ya yi lahani ga yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a farkon wannan wata.

Arangamar na zuwa ne sa’o’I kalilan bayan da MDD tayi Allah wadai da ci gaba da rashin mutunta takunkumin amfani da makamai da kasashe da dama suka kakabawa Libya.

Karya yarjejeniyar na faruwa ne a lokacin da bangarorin suka yi alkawarin mutunta takunkumin a gaban shugabannin duniya a wani taron kasa da kasa a Berlin na kasar Jamus a makon da ya gabata.

Kawuna sun rarrabu a Libya tsakanin gwamntoci masu gaba da juna a gabas da yammacin kasar, kana kowane bangare na samun goyon bayan kungiyoyin ‘yan bindiga da wasu kasashen waje.