Jigawa Ta Shirya Ba Yara Miliyan 1 Da Dubu 200 Rigakafin Polio

Gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa, yana hira a VOA

A zagayen bayarda maganin rigakafin Polio na watan Satumba da aka yi cikin makon da ya shige an hada har da tasoshin mota 86 a jihar
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce yara miliyan daya da dubu dari biyu ta shirya ba maganin rigakafin kamuwa da cutar shan inna, ko Polio, a zagayen watan Satumba na wannan aiki da aka yi a makon da ya shige.

Kwamishinan ayyukan kiwon lafiya na Jigawa, Dr. Abubakar Tafida, ya ce ya zamo tilas su kara azamar aikin a saboda an samu bullar sabbin kamuwa da cutar ta shan inna wasu jihohi makwabtan Jigawa.

Sai dai har yanzu ba a samu alkaluma na adadin wadanda aka samu nasarar ba su maganin a lokacin wannan aiki ba.

A yunkurinta na kara azamar kawar da wannan kwayar cuta ta Polio, gwamnatin jihar ta Jigawa ta girka karin masu bayar da maganin a tasoshin mota 86 cikin jihar domin tabbatar da cewa dukkan yara masu shigowa cikin jihar ko biyowa ta cikinta, sun samu wannan magani.

A lokacin wannan aikin na Satumba, an sanya malamai da sarakuna da kuma shugabannin kungiyar direbobi ta Najeriya cikin masu zaburar da mutane da kuma taimakawa wajen cimma nasarar aikin.