Jihar Bauchi Tayi Gangamin Yaki da Cutar HIV

Ranar Yaki Da Cutar HIV

A kowace ranar daya ga watan Disamba a shekara, ana gudanar da bukin ranar yaki da cutar HIV.
A kowace ranar daya ga watan Disamba a shekara, ana gudanar da bukin ranar yaki da cutar HIV. A jihar Bauchi an samu gudanar da irin wannan bukin.

Da yake bayani, shugaban hukumar yaki da cututuka kaman tarin fuka, kuturta, zazzabin cizon sauro, da kuma sida, Dr. Abdul-Aziz Manga, yace an samu raguwar cutar daga yadda take a shekarun baya zuwa yanzu.

Dr. Manga yace, “Wannan ranan an kebe ta ne sabili da tunawa da wadanda suka rasa rayukan su da wanan cutar.” Ya kara da cewa, dalilin kafa ranan nan shine saboda ya kara sa mutane kwazo wajen samo hanyoyin da za a yi jinyar wadanda suka kamu da cutar nan gaba.

Bayan haka kuma, Dr. Manga yace kiyaye ranar yaki da cutar HIV zata taimaka wajen wayar da kan jama’a su san yadda irin illar cutar ga jama’a a duniya.

Ga cikakken rahoton da wakiliyar Sashen Hausa ta hada.

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Yaki da Kwayar Cutar HIV - 3:49