Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Masu Matsuwa Suna Sa Wannan Matsalar Ga Jariransu


Ana duba yara a karamin asibiti dake kauyen Bagega a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya.
Ana duba yara a karamin asibiti dake kauyen Bagega a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya.

Wani sabon bincike ya nuna cewa jarirai da matan da suka sha wahala cikin rayuwarsu suka Haifa, zasu iya zama da wannan wahalar har cikin rayuwarsu ta manyantaka.

Wani sabon bincike ya nuna cewa jarirai da matan da suka sha wahala cikin rayuwarsu suka Haifa, zasu iya zama da wannan wahalar har cikin rayuwarsu ta manyantaka. Wannan ya samu ne a wata jaridar bincike mai suna Biological Psychiatry.

Masu bincike daga Jami’ar Haifa a kasar Isra’ila sunce binciken da akayi akan dabbobi da mutane, ya nuna cewa matan da suka sha wahala tun kamin suyi ciki zasu iya samun wannan matsalar ga jariransu.

A karshen shekarar da ta wuce, kungiyar yada labaran magunguna ta bada labari akan binciken da ya nuna cewa yaran da iyayen dake cikin matsuwa sosai suka haifa, sunfi samun matsalar wannan ciwon.

Wani binciken ya nuna cewa jariran da aka haifa ga mata wadanda suka sha wahala a rayuwarsu sunfi samun karuwar wahalar rayuwa da karuwar CRF1 (wata kwayar hallita da ta shafi damuwa da matsuwa) a lokacin haihuwa.

Har yanzu, masu bincike suna nan suna ta kokarin gano dalilin da yasa matsuwar iyaye ke haifar da wannan damuwar domin taimakawa al’umma ta nan gaba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG