Jihar Bauchi Zata Ba Jama'a Damar Fita a Ranakun Laraba da Asabar

Hukumomi a jihar Bauchi sun umurci jami’an tsaro akan su tabbata jama’a suna bin dokar hana fita, a wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus a fadin jihar.

A halin da ake ciki, an tabbatar da samun karin mutum guda wanda ke dauke da cutar coronavirus, yanzu adadin masu dauke da cutar ya kai mutum uku a jihar Bauchi.

A jawabin da ya yi wa manema labarai a daya daga cikin cibiyoyin da ake killace masu cutar COVID-19 a asibitin Bayara, shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus da kuma cutar Lassa Fever a jihar Bauchi, kuma mukaddashin gwamnan jihar Sanata Baba Tela, ya ce an gudanar da gwaje-gwaje 99 ya zuwa yanzu, kuma cikin mutane 23 da aka dawo da sakamakon gwajinsu, mutum daya ne aka tabbatar yana dauke da cutar coronavirus. Ya kuma ce an killace mutumin ana kuma sa ran sallamar sauran mutane biyu da aka killace a baya a cikin mako mai zuwa.

Baba Tela ya kara da cewa gwamnatin jihar zata ba mutane damar fita a ranakun Laraba da Asabar daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma don zuwa neman abinci da sauran abubuwan biyan bukata, amma ya zama dole mutane su kula da matakan nisantar juna da kuma wanke hannu. Ya kuma ce jami'an tsaron dake sintiri ba don su ci zarafin jama'a aka baza su ba, amma kuma duk wanda ya karya doka to ya kuka da kansa.

Ga karin bayani cikin sauti daga Abdulwahab Muhammed.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Bauchi Zata Ba Jama'a Damar Fita a Ranakun Laraba da Asabar