Jihar Damagaran a Nijar Tana Samun Damina Mai Albarka

Damina a Damagaran Arewacin Nijar ta yi kyau

Damina ta kankama a jihar Damagaran ta Jamhuriyar Nijar inda manoma suka yaba da yadda shuke-shuken da suka yi suke cigaba da tsirowa da girma da kyau ba kamar kudancin kasar ba.

Damina ta tsaya a sassa daban daban na jihar Damagaran dake Jamhuriyar Nijar lamarin da ya banbanta a abun dake faruwa a kudancin kasar.

Manoman jihar dai tuni suka yi nisa da harkokin noma kamar yadda wadanda abun ya shafa suka shaidawa Muryar Amurka.

Wani manomi Malam Sale yace damina bana sai godiya ga Allah saboda kawo yanzu ta yi kayau. Ya shuka hatsi da wake da gyada.

Wani yace koina aka duba a jihar gonaki sun yi kyau da fatan zasu cigaba hakan. Shi ko Adamu Muhammad cewa yayi suna ganin alamar zasu dace wannan shekarar.

Kwarin da kan jawo masu matsala babu su yanzu saidai a can kudancin kasar inda suke da labarin sun fara fitowa.

Manoman na anfani da takin gargajiya ne. Basu da takin zamani amma suna bukata.

Baicin maza manoma akwai mata kuma dake noman kubewa. Suna shuka kubewan ne ba domin yin miya da ita a gidajensu ba kawai, suna sayarwa su biya bukatun kansu da na iyalanasu.

Mace mai noman kubewa a Damagaran, Arewacin Nijar

Manoman sun yi kira ga gwamnati ta taimaka masu da taki da kayan aiki.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Damagaran a Nijar Ta Samun Damina Mai Albarka - 2' 35"