Jihar Kano Ta Bullo Da Wani Tsari Don Tabbatar Da Hana Bara

Biyo bayan dokar hana bara da gwamnatin jihar Kano ta yi, gwamnatin jihar ta kuma ce duk almajirin da ta kama yana bara a titi zata kama shi ta kai shi wasu makarantun kwana da ta bude a kananan hukumomi guda goma sha daya dake jihar.

A watan da ya gabata ne gwamnatin jihar kano ta hana bara da almajirai ke yi a bisa manyan tituna da ke fadin jihar da sunan neman ilimin addinin islama.

Gwamnan jihar ya ce matakin hana barar ya biyo bayan kudirin da suka dauka ne na tabbatar da ba kowa ilimi kyauta tun daga matakin firamare har zuwa sakandare.

Wani malamin irin wadannan makarantun, Alaramma Salisu Isa Dan Kwandarai, ya ce tsarin da gwamnati ta fito da shi ba wani sabon abu ba ne duk da cewa kowacce gwamnati da yadda take aiwatar da tsarinta, amma sun bar komai a hannun Allah.

Kwamishinan ilimin jihar Kano Muhammadu Sanusi Sa'idu Kiru, ya ce gwamnatin jihar ta hana yawon bara ne ba karatun allo ba kuma gwamnatin yanzu zata dinga biyan malaman dake da tsangayu a jihar duk wata ta kuma samar masu abinci don dalibansu da iyalansu ta yadda almajiran ba zasu fita bara ba, idan har suka amince da tsarin.

Shi kuma kwamishinan yada labaran jihar Kano Mohammadu Garba, ya ce wasu alkaluma sun nuna cewa kashi 60 zuwa 70 cikin 100 na almajiran dake bara a titi a jihar baki ne daga wasu jihohi har ma da kasashen waje.

Ga karin bayani cikin sauti daga Baraka Bashir.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Kano Ta Bullo Da Wani Tsari Don Tabbatar Da Hana Bara